Breaking News

Yunƙurin ceto kwaɗo mafi girma a duniya

 A lokacin da Cedrick Fogwan ya fara haduwa da wani kwado mai suna goliath, ya yi matukar farin ciki dangane da yanayin girman kwadon.


Kamar dai yadda ake daukar kanana yara, yace, yayi nasarar ceto kwadon.

Mutumin dan kasar Kamaru mai rajin kare halittu, yayi matukar nuna sha’awar bullo da Shirin yaki da barazanar bacewaar nau’ikan halittu daga doron kasa.

Yace "A lokacin da na fahimci wannan nau’in na dabam ne, shine mafi girma a duniya, sai nake cewa wannan wani abu ne da ba lallai a iya a samunsa a sauran wurare ba kuma ina alfahari da hakan,".

"Mazauna yankin sun ce, Allah yayi musu baiwa da samun wani abu kamar wannan, sun dangantashi da cewa wani muhimmin abu ne ga al’adunsu."

Girman Goliath frog ya kai na mage, wanda tsawonsa ya kai senti mita 32 yayin da nauyinsa ya zarce kilogram 3.25.

An shafe gomman shekaru ana farautar kwadin goliath a matsayin abinci da harkokin kasuwanci a kasashen Kamaru da Equatorial Guinea.

Koguna da koramu sune wuraren zama ga kwadin wanda ake yawan samun matsalolin lalatasu don haka a halin yanzu an ayyana kwadon da cewa yana cikin matsananciyar barazana.

Kwadon wanda masana kimiyya da mutanen kasar Kamaru ba su da masaniya mai yawa game da muhimmancin da yake dashi a fagen kare muhallin halittu, kamar cinye kwarin dake lalata amfanin gona.

Tawagar masu rajin kare halittu suna aikin janyo ra’ayin mafarauta don su shiga aikin kimimiyya, kamar nadar bayanan dake shafar rayuwar kwadin maimakon amfani da kwadin a matsayin abinci.

Sannan suna aiki da kungiyoyin alummar yankunan kasar domin samar musu da tsarin kiwon dodon kodi don maye gurbin kwadin a matsayin abinci.

Aikin kare nau’in halittun yana shirin mayar da kwadon goliath zuwa sabbin koguna dake lambun Mount Nlonako.

Kiran da wani tsohon mafarauci yayi na cewa a gabatar da kwadon wanda wani makwabcinsa ya kama shi ne mafarin aikin. Cedric yayi nasarar ceto kwadon kuma ya mayar dashi zuwa gandun daji.

Yace, “Nayi amanna zai cigaba da kasancewa namu har abada kuma zamu cigaba da yin alfahari dashi."

No comments