A wannnan makon za mu yi magana ne kan yadda ake gyaran gashi, saboda muhimmancin sa ga mace wajen kwalliya da jan hankalin ango.
Hakika maza sun sha banban wajen abin da ke burge su a jikin mace, amma yalwar gashi na burge da yawa daga cikin maza. Kuma abu ne sananne cewa, idan mace ba ta da yalwar gashi, ta kan ji rashin dadi, har ma ita kanta ta kan yi sha'awar mace 'yar uwarta mai yalwar gashi.
A wannan zamani akwai hanyoyin da za ki bi don gyaran gashinki, yadda gashinki zai kasance mai tsayi sheki da kuma laushi. Kuma za ki iya yin hakan cikin sauki. Dalilin da ya sa, mu ka rubuta wannan makala ke nan.
A yau za mu kawo hanyoyi 3 da mace za ta bi don gyara gashinta. Hanyoyi biyu na farko bayani ne a rubuce, yayin da mu ka wallafa faifai bidiyo domin yin bayanin hanya ta ukun, don ku ganewa idonku yadda aka yi bayani filla-filla kan wannan hadin. Da fatan a sha kataru lafiya.
1. Wannan man da za mu bayyana yadda ake hadawa, amfaninsa bai tsaya wajen gyaran gashi ba kadai, za'a iya amfani da shi wajen gyaran fata, don kiuwa baya da gyaran gashi man kan sanya fata ta yi laushi da sheki, yadda maigida zai ji dadin mu'amala da ke cikin annashiwa.
Kayan hadin da ake bukata.
1. Man kwakwa 1/2 na karamin kofi
2. Man kadanya 1 karamin kofi
3. Man habbatus sauda 1/4 karamin kofi
4. Zaitun lauz 1/4 karamin kofi
5. Ruwa 2/3 tukunya
6. Mixer
7. Tukunya
8. Cokali
9. Leda
Yadda ake hada Wannan mai.
Ana bukatar ki samu kwano mai tsafta, sai ki zuba man Habbatus saudarki da zaitun lauz da man kwakwa da na kadanyar duk a cikin wannan kwanon. Bayan kin zuba dukkan mayukanki cikin wannan kwanon sai ki zuba ruwa cikin tukunyarki ki dora kan wuta, daga nan sai ki sanya kwanonki mai dauke da mayukanki cikin tukunyar nan. Ko kin san dalilin yin haka, dalili anan shine, ba'a son dora mayukan a wuta kai tsaye, saboda gudun kar wasu muhimman sanadarai dake cikin man su kone.
Bayan kin sanya kwanon cikin tukunyar, sai ki dauko cokalinki ki rinka juyawa a hankali a hankali har sai mayukan sun gaurayu kuma sun narke sosai.
Bayan kin tabbatar da cewa, mayukan nan sun hadu sun narke gaba daya, sai ki sauke sannan ki rufe da ledarki mai tsafta, ki sanya a cikin firji, har sai ya fara daskarewa. Daga nan sai ki zuba a 'Mixer' ki yi ta gaurayawa, za ki ga ya hadu ya yi kyau sosai. Idan har ya hadu yadda ake so, za ki ga ya na Kamar kumfa kumfa, to ya hadu kenan.
Bayan ya hade Sosai sai ki juye wannan hadin manki cikin mazubinki mai kyau da ki ka tanada ki rufe. Kin kammala hada manki.
Za ki iya yin amfani da wannan man wajen Gyaran fata. Saboda kamar yadda mu ka ambata tun a farko ya na sa fata ta yi kyau da laushi. Hakanan, za ki iya amfani da shi don maganin narkanwa, ko waskane. Hakazalika, ya na hana bushewar fata, da tsagewar lebe. Sannan yana gyara Gashi ya sa ya yi tsayi, Baki, da kuma laushi.
2. Amfanin wannan hadin ya takaitu ga gyaran gashi ne kadai. Ga kayan hadi da kuma yadda za ki hada nan a kasa.
Kayan Hadin Da ake Bukata:
1. Kwai Guda 2.
2. Man Zaitun Babban Cokali 4.
3. Zuma Babban Cokali 1
4. Man Kwakwa Babban Cokali 3
Da farko sai ki samu mazubinki mai tsafta, ki zuba man zaitun, da zuma sannan sai ki fasa kwanki ki zuba, ki gauraya da kyau, har sai kin tabbatar sun cakudu so sai.
Kafin yin wannan hadin ki tabbatar kin tsefe kan ki. Sai ki shafe gashinki tun daga matsirarsa , sannan sai ki rufe kanki da hular leda ki jira tsawon awa guda.
Daga nan sai ki wanke kan da man shampo, sannan ki sake shafe gashinki tun daga matsirarsa da man kwakwarki da ki ka tanada tun da farko, ki sake rufewa da hular leda tsawon awowi 6 zuwa 8.
Bayan wannan lokacin sai ki tsefe gashin za ki sha mamaki, don kuwa idan ki ka lura tsayinsa zai karu, kuma zai kasance mai sheki da kuma taushi.
Fadakarwa: Za ki aikata haka sau daya a sati. Kuma dangane yawan kayan hadin da mu ka ambata a sama ya danganta da yawan gashinki ko akasin haka, don haka za ki iya rage ko kara yawan kayan hadin gwargwadon bukatarki.
3. Kamar yadda mu ka ambata a sama bayan mun kammala da hanyoyi biyu na farko, ga bidiyon da zai mi ki bayanin yadda za ki yi hadi na ukun. A sha kallo lafiya.
Gyaran Gashi: Yadda Za Ki Gyara Gashinki Ya Kasance Mai tsayi, Sheki Da Laushi
Reviewed by lafiyar iyali
on
January 13, 2019
Rating: 5
No comments