Barkan mu da wannan lokaci, fatan kuna cikin koshin lafiya. Matsalar saurin kawowa maniyyi yayin jima'i da maza kan yi, matsala ce da ke addabar mutane da dama, sai dai abin farin cikin shine akwai hanyoyin magance wannan matsala.
Kamar yadda bincike ya nuna akasarin maza sun kan riga mata yin inzali yayin jima'i, to amma ba anan gizon ke sakar ba, wasu mazan su kan kawo maniyyi da zarar sun fara saduwa da iyali. Babban abin takaicin shine, yayin da shi ya yi inzali, a lokacin ne matar ke da bukatar sa, saboda ita ba ta yi inzalin ba, wanda hakan kan haifar da matsala a zamantakewar aurensu.
Saurin inzali kan haddasa babbar matsala a zamantakewar aure, inda za ka ga maigida na yiwa amarya ko uwargida magana amma sai ta yi biris da shi kamar ba ta ji me ya ke fada ba, ballantana ta kula shi saboda tuni raini ya shiga tsakaninsu sakamakon kasa biya ma ta bukata.
A wannan makala za mu yi kokarin kawo wa mai karatu hanyoyin magance wannan matsala ta saurin inzali kamar yadda binciken masana kiwom lafiya ya tabbatar.
Sai dai zai yi kyau mu yi tsokaci kan abubuwan da ke haddasa saurin inzali ga mazaje, hakan shi zai kara haske kan yadda wannan matsala ta ke. Saboda ba lallai ne, abin da ya haddasa wa wani matsalar saurin inzali ya yi daidai da ta wani ba.
Abubuwan da kan haifar da matsalar saurin inzali na da yawa amma, wadanda su ka fi shahara sune:
1. Sabon Shiga.
Idan mutum sabon shiga ne,barawo da sallama, Inji hausawa. Ga dukkan alamu wannan baya bukatar karin bayani. Amma dai muna nufin ango farkon aure. Kasancewar sa sabo ga al'amarin jima'i bai san yadda zai mallaki kansa ba yayin saduwa da amarya.
2. Matsananciyar Damuwa.
Idan mutum ya samu kansa cikin damuwa, sakamakon al'amuran rayuwa ko kuma damuwar ta kasance tsakanin sa da amarya ko uwargida. Hakan kan haifar masa da matsalar saurin inzali. Wannan kuwa ya hada da damuwa akan basussuka, gidan haya, matsalolin iyali,rashin lafiyar makusanci,durkushewar kasuwanci da dai sauran matsalolin rayuwa.
Idan magidanci ya dauki lokaci mai tsawo ba tare da ya sadu da iyali ba, hakan kan haifar masa da saurin inzali.
4. Tsoro.
A duk lokacin da mai gida ya jewa iyali a lokacin da yake tsoron wani abu a rayuwa, ko kuma ya karaya akan ba zai iya biya mata bukata ba, to labudda yana iya kawo maniyyi da wuri.
5. Zumudi.
Wani lokacin idan mutum ya kasa mallakar kansa game da jima'i, saboda wani dalili to zai iya kawowa maniyyi da wuri.
6. Gaggawa Yayin Jima'i.
Wanan na nufin mai gida ya dinga kaiwa da komowa cikin sauri a yayin jima'i. Ba shakka hakan na sabbaba saurin inzali.
Kullum dai muna fadar abincinka maganinka,masana na yawaita bada muhimmanci akan abincin da muke ci don kuwa shi ya shafi dukkan al'amuran lafiyarmu ne.
8. Gajiya.
Yayin da mutum ya yi aiki mai wahala ya gaji sosai, masanan sun ce hakan kan haifar ma sa da wannan matsala ta saurin inzali.
Idan mutum ya kasance ba ya motsa jiki ko yin wani aiki da zai sanya jinin jikinsa ya tsinke don ya kewaya sosai, zai iya fukantar matsalar saurin inzali.
Fadakarwa: Idan dalilan da su ka haifar da saurin inzali ga mutum sun kasance cututtuka ne, ko kuma matsalar da aka haifi mutum da ita. Ita kam irin wannan ba makawa sai mai fama da daya daga cikin abin da mu ka ambata, ya ga likita don samun mafita.
Misali ga wadanda wata cuta ce ta haddasa ma sa saurin inzali, to samun waraka daga wannan cutar shine maganin saurin inzalin da ya ke yi. Yadda za ku fahimci lamarin shine, ana danganta ciwon sanyi ko basir da raunin mazakuta da saurin inzali, ga duk mai fama da irin wannan matsala da zarar ya warke daga ciwon sanyin ko basir din, da iznin Allah karshen matsalarsa ta saurin kawo ruwan maniyyi ta kare.
Hanyoyin Magance Saurin Inzali.
Babban abin farin ciki game da wannan matsala shine, ana samun bakin zaren cikin sauki matukar dai ango ko magidanci zai bi shawarwarin masana.
Bayan haka ana bukatar hadin kan ma'auratan biyu don magance saurin inzali. Ba batun kunya a wannan fage.
Yana da kyau ango ko mai gida ya san cewa maza sun fi saurin yin inzali idan aka kwatanta su da mata, wannan yasa ya zama dole a gabatar da wasa kafin saduwa don a motsar mata da sha'awrta yadda za ku zo dai-dai lokacin inzali.
Ta yiwu wasu sun san yadda za su motsa sha'awar mace amma saboda sabin angwaye za mu kawo bayani a takaice.
Masana na ganin wasa kan fara ne tun daga maganganun fatar baki, kamar yabon irin kyaunta ko kwalliyarta da wasu kalamai da za su nuna kana sha'awar ta.
Idan an himmatu da yin jima'i akwai guraren da mace ta ke da matukar son a taba a jikin ta,ba don komai ba sai don suna da jijiyoyi da ke kaiwa kwakwalwa sakon jin dadi da sauri.
Ango zai mai da hankali wajen wasa da nononta sosai zai fara sannu a hankali, tun daga shafawa yana mulmula kansa,har ya kai bakinsa yana tsotsa..............
Sai gaban ta, a gaban ta kuma abin da ake kira da dan tsaka yin wasa da shi na saurin birkita mace. Don hakaa sai a kula ai wasa da shi ainun idan da halima a tsotse shi da baki.......
Daga nan za'a iya amfani da dan yatsa a saka cikin farji. Ai wasa dashi sosai. To wannan zai sa ta birkice.To anan sai ango ya lura a yayin da yaga ta birkice sosai tana bukatar sa, a wannan lokacin ne zai je mata, kuma hakan shi zai bayu ya zuwa ganin sun zo tare.
Idan kuma har ya riga ta, to ta yiwu itama ta kusa, kuma mun san ba da zarar namiji yayi inzali gabansa ya ke kwantawa ba,to zai raka ta kadan yana kaiwa yana komowa har itama ta biya bukatar ta.
Sai dai dole ne ango ya lura da inda yafi sa matarsa jin dadi don kuwa matan sun sha bambam. Inda zaka tabawa wata ta ji dadi ba lalle ne in ka tabawa wata za ta ji dadi ba.
Idan har mutum na da saurin inzali,to yayin da suke wasa shi kuwa sai ya guji goga gabansa a jikinta hakanan kuma ita matar kar ta yi masa wasan. Ma'ana kar ta shafa ko taba gabansa har yayin da za su sadu.
3. Tsayawa Yayin Da Ake Jima'i.
A yayin da suke jima'i idan ya ji alamar zai yi inzali sai su dakata da abin da suke, hakan ya hada da daina motsi zuwa wani lokaci har sai ya ji ya koma, sai su ci gaba. Haka zai dinga yi har sai ya ga alamar ita kuma za tayi inzalin sai su yi tare ko ma ta riga shi. Saboda da wannan dalilin ne muka ambata a baya cewa al'amarin na bukatar hadin kan ma'auratan a junan su.
4. Motsa Jiki.
Bincike ya tabbatar da cewa motsa jiki da ya hada da sassarfa, gudu, da sauran wasannin motsa jiki na taimakawa mai wannan matsala ya samu waraka.
Yadda ma'aurata za su kwanta na da tasiri ta fuskar inzali. Bincike ya nuna amarya ta hau kan ango zai bayu zuwa ga saurin kawowarta. Ka ga idan haka ne, to lalle irin wannan kwanciya za ta taimakawa mai saurin inzali.
Wannan hanyar na bukatar gwaji, idan an dace, to an samu mafita.
6. Jan Nunfashi Sannan A Sake Shi.
Mun fada a sama cewa dakatawa na kara tsawon lokacin kawowa. Hakanan a yayin da ake cikin jima'i sai a ja nunfashi ta hanci sosai ya shiga cikin ciki, sai a sake shi a hankali. Wannan ma na kawo jinkirin inzali.
7. Yin Jima'i A Hankali.
Ango ko mai gida ya guji gaggawa a yayin da yake jima'i da iyali. Abin nufi yayin da namiji ke kaiwa da komowa a kan iyali to yayi hakan a hankali,don kuwa zuwa da dawowa da saurin kan haifar da inzali ba tare da ka shirya ba.
Akwai dangogin abinci ma su gina jiki da ke taimaka wa ma'aurata samun gamsuwar jima'a. Mu na fatan yin rubutu a kansu, amma kafin lokacin, misalin irin wadannan nau'ikan abinci sun hada da, kayan marmari, ganyayyaki, kwai, kabewa ko 'ya'yanta da sauran su.
Mu na fata masu fama da wannan matsala za su jarraba wadannan hanyoyi don samu waraka daga wannan matsala mai tarwatsa rayuwar aure, kuma muna addu'a Allah Ya sa sanadiyar mu ne za su samu kubuta daga wannan matsala,amin.
A karshe muke tabbatarwa da ango ko magidanci cewa da zarar wannan matsala ta kau, hakika za ka ga canji, rayuwar aurenku za ta koma abar alfahari wacce ke cike da farin ciki,shakuwa da kuwa matsananciyar kauna.
https://mynovels.com.ng/abubuwan-da-ke-haifar-da-raunin-mazakuta/
ReplyDelete