Dabino shahararren da itaciya a Duniya ba ga masu karatu ba kadai. Haka nan, mu na kyautata zaton mai karatu ya san da cewa, shi dabino ya sha bam-bam wajen girmansa, launinsa da kuma dandanonsa (zakinsa). Ana yin amfani da danye ko busasshen dabino,gwargwadon bukata. Ko dai a wanne irin yanayi akai amfani da shi ya na dauke da sanadarai masu matukar muhimmanci wajen inganta lafiyarmu.
Mafi yawan mutane suna cin dabino ne don zakinsa, ba tare da sanin amfaninsa ga lafiyarsu ba. To sai dai dabino na da matukar fa'ida ga lafiyar jikin bil'adama.
Binciken masanan zamani ya nuna yawan cin dabino ga maza yana kara mu su karfin sha'awa da kuma karfin mazakuta. Wasu masana sun shaidawa jaridar 'Premium Times' cewa, yin amfani da dabino ga maza na kara musu karfin sha'awa da kuma karfin mazakuta. Dr Aminu Kareem ya shaidawa jaridar cewa, yawan cin dabino ga maza da ke da matsalar gamsar da iyali, na iya magance musu wannan matsala sannu kan hankali.
Saboda haka ne, mu ke son amfani da wannan dama don kawowa ma su karatu irin dibim baiwar da ALLAH(S.W.T.) yai wa wannan dan itaciya ga lafiyar al'umma.
1. Karfin Mazakuta.
Kamar yadda muka fara ambatawa tun da farko, bincike ya nuna cewa dabino na kara karfin mazakuta. Don samun sakamako mai kyau, a zuba dabino cikin nonon awaki ya kwana, sai a nike shi a hada da nonon da aka cire shi daga ciki a hada da zuma a sha.
Wata hanyar kuma ita ce, a samu dabino kamar cikin tafin hannu, ko kuma guda 9 ko goma 13, sai a cire kwallon a zuba a ruwa ya samu kamar awa biyu ko uku,a markade shi a zuba madara gwangwani daya da zuma cokali uku a sha sau daya a kullum.
2. Cushewar Ciki.
Dabino yana magance matsalar cushewar ciki, saboda yana kunshe da sinadarin da ake kira "Soluble fibre" a turance. Shi kuwa wannan sinadari yana taimakawa wajen kewayawar abinci a cikin hanji cikin sauki.
Yadda za'a iya magance wannan matsala da dabino shine, Mutum ya samu dabino kamar guda 7 zuwa 15, sai ya zuba su cikin ruwa su kwana, idan gari ya waye sai ya tsame su daga cikin ruwan ya cinye. Yin haka akai-akai zai sanya cikinka ya kasance cikin koshin lafiya, sannan ya hana ka samun matsalar cushewar ciki.
3. Karfin Qashi.
Saboda dabino na kunshe da sanadaran selenium, manganese, copper da kuma magnesium ya ke kara karfin qashin dan adam. Su wadannan sinadarai da aka ambata a sama suna da matukar muhimmanci wajen ginin qashi.
Abu ne sananne cewa a lokacin da mutum ke kara manyanta qashinsa na kara rauni, don haka cin dabino akai-akai zai taimaka wajen ginawa da kuma qara masa qarfin qashi.
Kasancewar dabino na kunshe da sinadaran suger, proteins da kuma nau'ikan vitamins yasa shi taimakawa wajen ginin jiki. Yawan cin dabino gami da kokumba na bada sakamako da sauri.
5. Karin Kuzari.
Masana sun tabbatar da cewa dabino na dauke da nau'ikan suger kamar glucose, fructose da sucrose, wannan ya sa shi zamowa dan itace mai matukar amfani wajen karin kuzari. Saboda haka ne ma ya sa mutanen da suka fahimci hakan ke ci dabino da zarar sun ji alamun kasala.
Haka nan ma mutanen da su gudanar da wani aikin karfi ko motsa jiki suka gaji,suke cin dabino don samun wartsakewa da gaggawa.
Dabino na kunshe da sanadarin da ake kira potassium da turanci, wanda bincike ya nuna cewa yana rage hadarin bugawar zuciya, da sauran cututtukan da suke shafar zuciya.
Don samun biyan bukata a zuba dabino guda bakwai ko tara a cikin ruwa, a fitar a ci bayan awa uku sau biyu a mako.
7. Karfin Ido.
Shi dai dabino na dauke da sinadarin vitamin A wanda ya ke taimakawa wajen kara karfin ido. Don haka sai a yawaita cin dabino don samun karfin ido.
8. Sauqin Haihuwa Ga Mata Ma Su Juna Biyu.
Yawaita cin dabino ga matan dake da juna biyu na taimaka mu su wajen samun sauqi lokacin da haihuwa ta zo mu su. Wani binciken kimiyya da masana kiwon lafiya su ka gudanar kan hakan, ya nuna cewa, cin dabino ga mace mai juna biyu, a kowacce rana har tsawon makonni 4 kafin ta haihu ya na taimakawa ta samu sauqin haihuwa, da yardar Allah Madaukaki.
Dabino na karawa dan-adam kaifin basira, saboda ya na kunshe da sinadaran 'vitamins' musamman rukunin B6, mai yawan gaske a cikinsa, wanda ya ke da tasiri sosai wajen qara inganta lafiyar kwakwalwa hakan kuma sai ya haifarwa mutum kaifin basira.
Wannan ita ce tsarabar da wannan shafi na Lafiyar Iyali ya kawo mu ku a wannan rana, mu na fatan za ku jarraba don samun wadannan fa'idoji na dabino. Hakanan, mu na kira ga al'umma duk wanda ya san wasu magungunan da dabino ke yi ga lafiyar dan-adam sai ya sanar da mu don karuwar 'yan uwa Musulmi, za ku iya aiko ma na da sakonninku ta hanyar "Comment" game da wannan makala.
No comments