Breaking News

Amfanin Kabewa Ga Lafiyar Dan-adam Da Ba Kowa Ya Sani Ba









Wani mai hikmar magana na cewa, "Abincinka ya kasance maganinika, kuma ka mayar da maganinka abincinka". Mafi yawan mu ba mu dauki abincin da muke ci a matsayin magani ba, amma wannan kuskure ne. Shi abinci da Allah(S.W.T) Ya samar ma na don mu ci mu rayu, Ya cusa wasu sanadarai a ciukinsa da jikinmu ke bukata don ya ginu kuma ya kasance cikin koshin lafiya.

Wannan dalili ne ya sa wannan shafi na Lafiyar Iyali ya himmatu wajen zakulo amfanin da abinci da mu ke ci ke yi wajen inganta lafiyarmu, wanda idan mai karatu ya yi amfani zai ga fa'idar abin.

To a yau mun zabi mu yi magana kan amfanin kabewa ga lafiyar dan adam. Saboda haka mun zakulo wani sakamakon bincike ga shi mun waallafa don amfaninku. Da fatan za ayi karatu lafiya, Allah Ya sa mu dace, amin.

Sai dai kafin mu fara bayyanawa mai karatu amfanin kabewa ga lafiyar dan adam, zai yi kyau mu kawo ma ka, irin tarin sanadaran gina jiki da Allah Ya yi kabewa baiwa da su. Wani bincike da manazarta su ka gudanar, kuma aka wallafa a wani shafin yanar gizo mai suna "Health Line" ya nuna cewa kabewa na kunshe da sanadaran, Protein da Carbohydrate da Fiber da Vitamin A da Vitamin C da Potassium da Copper da Manganese da Vitamin B2 da Vitamin E da kuma Iron.

Hakanan masana sun bayyana cewa, kabewa na kunshe da wannan sanadaran amma ba su taka kara sun karya ba, sanadaran sune, magnesium da phosphorus da zinc da kuma folate. Sai dai duk da haka cin kabewar zai iya samrwa mutum wani adadi na wadannan sandarai wadanda suna da tasiri ga lafiyar jikin bil'adama.

Daga cikin amfanin kabewa ga lafiyar dan adama akwai:


1. Inganta Lafiyar Zuciya

Sinadaran potassium da Vitamin C da na Fiber, da Allah ya albarkaci kabewa da su,  na taimakawa wajen baiwa zuciya riga kafin kamuwa daga cututtukan da kan shafi zuciya. Hakanan akwai wani sanadari na maganesium da ta ke da shi. Sai dai kamar yadda masanan su ka bayyana ana samun wannan sanadari a kwallon kabewar, saboda haka mutum zai samu wannan alfanu na amfanin kabewa ne idan zai ci kwallonta, musamman ace mutum ya samu 1/3 wato (daya bisa uku) na kofi, ya ci a kowacce rana. Babu wata matsala wajen cin 'ya'yan kabewa, saboda ba su da wani dandano marar dadi, hasali ma gardi ne da su.



.2. Bunkasa Garkuwar Jikin Dan-adam

Allah Ya yi wa kabewa bai wa da wani sandarin 'beta carotene' da jikinmu ke mai da shi ya koma sanadarin Vitamin A, bayan mun ci kabewa ke nan. To shi wannan sandari ya na kara karfin garkuwar jiki.

Tun a farkon wannan makala mun bayyana cewa, Allah Ya yiwa kabewa baiwar sanadaran da ake kira da zinc da iron da folate da kuma Vitamin E, a turance. Su wadannan sandarai na ba da gagarumar gudunmawa wajen inganta lafiyarmu ta hanyar bunkasa wa ko karawa garkuwar jikinmu karfi. Mun san kuma ita garkuwar jikinmu ce ke da alhakin bai wa jiki kariya daga kwayoyin cutar da ke kawo wa jiki farmaki.

3. Saurin Warkewar Rauni.

Kabewa na kunshe da sanadarin Vitamin C mai yawan gaske a cikinta, kamar yadda mu ka fada a sama. Shi wannan sanadari na Vitamin C, na taimaka wa wajen kara adadin kwayoyin halittar jini da ake kira "White blood cell" da turanci wanda shi kuma ke kara karfafa tsarin garkuwar jiki da za ta haifar saurin warkewar rauni.

4. lafiyar Ido

Idan mai karatu bai manta ba a sama mun yi maganar sanadarin 'beta-carotene' da jiki ke samar da Vitamin A daga gare shi. Baya ga aikin Vitamin A da mu ka ambaata a sama, hakanan Vitamin A na taimaka wa wajen inganta lafiyar ido kuma ya kara karfin gani.

Bincike ya nuna cewa, rashin sanadarin vitamin A ko karancinsa a jiki ne ke haddasa, raunin gani ko ma mutum ya makance baki daya. Sakamakon haka tun da kabewa na da wannan sanadari ba shakka za ta taimaka wajen inganta lafiyar ido da karewa mutum daga makanta ko raunin gani.

Hakanan dai kabewa na da sandaran Vitamin C da E ma su yawan, wadanda ke wani aiki mai ban sha'awa a jiki, inda za su iya bai wa kwayoyin halittar ido kariya daga lalacewa.

5. Kabewa Na Rage Kiba/Teba

Duk da cewa, kabewa na dauke da snadaran gina jiki ma su yawa, amma duk da haka ta na da karancin sandarin 'Calories', saboda haka ne ya sa, masana ke lissafa kabewa cikin dangin abince mai rage kiba. Masana sun ce, mutum zai iya cin kabewa da yawa, kuma cin ta da yawan ba zai haifar ma sa da girman tumbi ba.

6. Gyaran Fata

Ba shakka kabewa na gyara fatar jiki ta shi laushi da haske. Baya ga haka wasu da su ka san aikin kabewa kan fata na yi mata kirari da "Mai da tsohuwa yarinya", saboda yadda matukar mutum ya lizamci shan kabewa, to shekarunsa ba za su nuna a jikinsa ba.

Na taba karanta wannan batun a wani shafin yanar gizo, amma sai na dauki abin kamar al'mara. Wata rana na kai ziyara wajen wani abokina mai sayar da kayan miya, sai na tarar su na cinikin kabewa da wata matashiya. Bayan ta tafi sai na tambaye shi abin da za ta yi da kabewar, ganin cewa kabewar katuwa ce kuma ban ga ta hada da sauran kayan hadin taushe ba, balle na ce ko biki su ke.

Abokina ya ban amsar cewa, wannan ita ce al'adarta, ta kan sayi kabewa da yawa kuma bayan lokaci kankani sai ta dawo ta ce har ta kare. Shi ma abin ya ba shi mamaki. Ya shaida min wata rana ya tambaye ta abin da ta ke yi da kabewa. Amsar da ta ba shi ita ce,a ganinka na kai shekara nawa, sai ya ce ba ta fi shekara 25 sai ta yi dariya ta ce, shekarunta sun kai talatin da doriya. A karshe ta ce, aikin da kabewar ke ma ta kenan.

Ya kara tambayar ta yadda ta ke sarrafa kabewar, sai ta ce, ta na dafa kabewar ne, ta na ci, amma ta kan hada da wasu kayan miya da allayyaho da za su kara mata dandano.

To me karatu ka ji aikin kabewa wajen gyara fata da inganta lafiyar dan adam, da fatan za a jarraba, kuma Allah Ya sa mu dace, amin.

7. Kuzarin Jiki

Har ila yau, daga cikin amfanin kabewa ga lafiyar dan adam akwai samarwa da jiki kuzari. Idan ka na son samun wannan fa'ida ta kabewa ga yadda za ka/ki yi. Ka samu kabewa ka fere ta ka yayyanka sannan ka markada ta sai ka hada da Goba ko Ayaba ka tace ka dinga sha lokaci zuwa lokaci. Wannan hadin  na taimakawa wajen kara kuzari ga jiki da maganin gajiya.


8. Karfin Mazakuta

Ba shakka yawan shan kabewa na kara wa namiji karfin mazakuta sannan yana inganta maniyyi da kara yawansa a jikinmu. Baya ga haka an bayyana cewa, shan kabewa na hana saurin kawowa yayin saduwar aure.

Domin samun wannan amfani na kabewa sai mutum ya samu kabewa ya yi miyarta da alayyaho, amma kabewar ta kasance ta na da yawa. 

No comments