Breaking News

Amfanin Man Zaitun Ga Lafiyar Bil'adama






1.  Daga cikin amfanin man zaitun ga lafiyar dan adam; Man zaitun na ƙunshe da sanadarin bitamin E, wanda ke inganta lafiyar fatar jiki ta hanyar hana ta kamuwa daga wasu cututtukan fata, kuraje, saboda haka sai mutum ya zauna lafiya.

Akwai wani hadi da ake yi da man zaitun da zuma da kuma 'yogurt', an fahimci cewa, man zaitun na inganta lafiyar fata, yayin da zuma da kuma 'yogurt' ke sanya fata ta kasance mai laushi. Matukar ki/ka yi amfani da wannan hadi na man zaitun za ki/ka samu fata mai kyau sheki da kuma laushi.

Abubuwan da Ka/ki ke Bukata

A. 1/3 na kofin yogurt
B. 1/4 na kofin zuma
C. Karamin cokali 2  na man zaitun

Yadda mutum zai hada wannan hadi na man zaitun kuwa abu ne mai sauki, Ka zuba man zaitun kan 'yogurt' ka gauraya su sosai, sannan sai ka kawo zumarka-ana son zumarka ta kasance mai kyau marar algus- ka hada ta kan man zaitun da yogurt da ka gauraya tun da farko, bayan ka zuba ta sai ka sake gauraya ta, za ka ga hadi ya zama mai kauri.

Yadda za ka/ki yi mafani da wannan hadi shine, ka/ki shafe fuskarki/ka da shi ka bar shi tsawon mintuna 20, sannan ka wanke da ruwan dumi.

Zaka iya yin amfani da wannan hadi na man zaitun sau ɗaya a mako.

2. Kamar yadda mu ka fada a sama, man zaitun na ƙunshe da sanadarin bitamin E, wanda ke aiki a matsayin 'antioxidant' da ke kare fata daga wasu abubuwa ma su haddasa bushewar fatar kamar yawan zafin rana da matsananciyar iska.  Amfani da man zaitun akan fatarmu na ba ta cikakken damshi tsawon lokaci, wanda kuma ya dace da kowacce irin fata.

Abin da Ka/ki ke Bukata

Man zaitun mai kyau, kadai

Abin da za ka yi shine, bayan ka fito daga wanka, sai ka jira ka tsane kadan, amma ba sai fatarka ta bushe sosai ba, sannan ka shafa man zaitun a fuskarka. Za ka bar shi a fuskarka kimanin mintuna 15, sannan ka wanke da ruwan dumi.

Abin Lura: Idan har bushewar fatarka/ki ya yi tsanani, za ka/ki iya amfani da man zaitun ta hanyar shafa shi a fuskarka/ki kafin ka/ki kwanta, ka bar shi har gari ya waye.  Idan gari ya waye sai ka wanke man zaitun din da safe tare da ruwan dumi.

3. Hana Yankwanewar Fata

Hakanan, yana daga cikin amfanin man zaiotun ga inganta lafiyarmu, hana yankwanewar fata da ke nuna alamar tsufa. Yayin da mutum ke kara yawan shekaru, hakanan shekarunsa ke nunawa kan fatarsa, sai ka ga ta fara tattarewa da yankwanewa. Zaka/ki iya jinkirta waɗannan alamun tsufan fata da man zaitun.

Abin da Ka/ki ke Bukata

Karamin cokali 2 na man zaitun
Karamin cokali 1 na ruwan lemon tsami
Gishiri dan kadan

Yadda za ka yi amfani man zaitun a wannan hanya don hana fatarka yamushewa shine, Ka shafe fuskarka da man zaitun zallar sa ba tare da ka hada shi da komai ba. Sannan sai ka hada sauran man zaitun da ya rage da gishirin, bayan ka gauraye su, sai ka zuba ruwan lemon tsaminka da tuni ka tanada ka kara gaurayawa, sannan ka kara shafe fuskarka/ki da wannan hadi, bayan mintuna sai ka wanke da ruwan dumi.

4. Gogewa Kwalliyar Fuska

Ana amfani da man zaitun wajen gogewa kwalliya a fuskar mata cikin sauki. Wani lokacin wasu daga cikin kayan kwalliyar mata kan yi wahalar fita. Idan ki ka samu kanki a irin wannan hali, abu ne mai sauki ki goge kwalliyarki da taimakon man zaitun. Yadda za ki yi shine ki samu man zaitun mai kyau sai ki diga man a kan kyallenki mai tsafta ki goge wajen da kwalliyar ta ke.

5. Maganin Fason Kafa

Yayin da fason kafa ya takura ma ka, yi amfani da man zaitun don samun sauki cikin gaggawa. Yi  amfani da ruwan lemun tsami cikin ruwan dumi ka wanke kafarka da kyau sannan sai ka shafe kafarka da man zaitun yadda kafar za ta kasance mai laushi da kuma santsi. Daga nan sai ka sa safar kafa don samun sakamako mai kyau kuma cikin sauri. Hakanan za ka iya yin yadda mu ka fada da dare idan za ka kwanta, sai ka sa kafarka cikin safa, idan gari ya waye za ka ga yadda kafarka za ta koma.

6. Man zaitun Na Kara Karfin Garkuwar Jiki

Ba shakka masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, man zaitun na karfafa garkuwar jikin dan-adam yadda da ta iya fafatawa da kwayoyin cutar da ke kai wa jiki farmaki kuma ta fatattake su. Mun sani, matukar kwayoyin cututtuka su ka samu gindin zama a cikin jiki, suke haddasa matsalolin lafiya da yawan gaske, to idan garkuwar jiki na da karfi ba ta yadda wadannan kwayoyin za su rayu cikin jiki ballantaba har su iya yaduwa su haifar da wata cuta.

7. Man Zaitun Na Bada Kariya Daga Cututtukan Zuciya

Amfani da man zaitun na taimakawa wajen rage yawan sinadarin kolestirol, wanda mun sani idan kwalastaral yayi yawa a cikin jini na haifar da illoli ga lafiya, wasu daga cikin irin wadannan matsaloli sun hada da wasu cutuka na zuciya.

8. Ana Amfani Da Man Zaitun Wajen Gyaran Gashi

Man zaitun na da amfani wajen gyaran gashi, musamman idan aka hada shi da wasu sinadaran. man zaitun na iya samar da sakamako mai ban al'ajabi saboda yadda ya ke inganta lafiyar gashi ya kiyaye gashin daga karyewa ko zubewa, sannan gashin ya kasance mai yalwa,tsayi, laushi da kuma sheki.

Domin samun gashi mai siffar da mu ka ambata a sama, mace za ta iya amfani da wani hadin man zaitun da muke son bayyanawa a kasa. Ana yin wannan hadi ne da man zaitun, da zuma da kuma kwaiduwar kwai.

Shi dai man zaitun, mai ne dake kunshe da sandarin bitamin E wanda ke taimakawa wajen hana zubewar gashi. Yayin da ita kuma zuma na hana bushewar gashi. Har ila yau zuma ta ƙunshi wasu sanadaran gina jiki kamar magnesium, zinc, sulfur, calcium, da kuma Bitamins waɗandake taimakawa wajen kara yawan gashi. Gwaiduwar kwai na cike da sanadarin furotin, mai gina jiki wanda kuma shine tushen farko na samar da yalwar gashi.

Abubuwan da ake Bukata

1/2 na karamin kofin man zaitun
Karamin cokali 2 na zuma
Gwaiduwar kwai guda 1

Yadda za ki hada wannan hadi na man zaitun

Tun da farko ki kada kwaiduwar kwanki sannan sai ki zuba zumarki a kanta ki gauraya su gaurayu sosai, daga bisani sai ki zuba man zaitun a kan su, ki sake gauraya wa sosai har sai kin tabbatar sun hadu yadda ya kamata. Daga nan sai ki zuba wannan hadi cikin kyakkyawan mazubi ki adana.

Yadda za ki yi amfani da wannan hadi na man zaitun

Za ki shafe gashinki gaba daya, ki tabbatar ko ina ya samu, tun daga tushen gashin, sannan ki  bar shi a kanki kimanin minti 20. Bayan minti 20 sai ki wanke da ruwan dumi, idan kina bukata sai ki shafe gashinki da kwandishana.

9. Man Zaitun Na Taimaka Wajen Hana  Kamuwa Da Ciwon Daji

Masana sun tabbatar da cewa, a kwai kyakkyawar alaka tsakanin amfani da man zaitun da kuma riga-kafin ciwon daji. Wasu mutane za su iya mamakin yadda al'amarin yake. Amma, ma su nazari kan dangantaka tsakanin abincin da muke ci yau da kullum da kuma lafiyarmu, sun tabbatar da cewa, amfani da man zaitun a abinci na iya taimakawa wajen riga-kafin kamuwa da ciwon dajin mama(Breast cancer).

A wani binciken da aka gudanar a kasar Saudi Arabia, an gano cewa wani sanadari mai suna 'oleuropein', wanda ake samu a ganyen zaitun, yana da magungunan ciwon dajin mama.

Hakanan, a wani gwaji da aka gudanar a kasar Spain, an gano cewa matan da suke yawan cin abincin da ke dauke da man zaitun, na samun riga-kafin kamuwa da ciwon dajin mama har  kimanin kashi 62 cikin 100, idan aka kwatanta da matan da ba sa amfani da man zaitun.

 10. Man Zaitun Na Taimaka Wajen Hana Kamuwa Da Ciwon Siga

Daga cikin amfanin man zaitun ga lafiyar dan adam, har da yadda ya ke taimakawa wajen riga-kafin kamuwa da ciwon siga. Yawan sanya man zaitun a cikin abincinka zai iya daidaita sigan dake cikin jininka. An samu bincike ma su yawan gaske da ke tabbatar da wannan amfani na man zaitun.

Bisa wani sakamakon bincike da Cibiyar Kiwon Lafiyar Jama'a ta Harvard, ta fitar ya nuna cin abinci mai ƙunshe da sandarin 'mono' da 'polyunsaturated fats', wadanda ke ƙunshe cikin man zaitun, zai iya taimakawa wajen hana kamuwa da ciwon siga.

Hakazalika, an gudanar da wani bincike, kuma aka wallafa shi a mujallar 'The American Journal of Clinical Nutrition' ya nuna, yadda amfani da man zaitun ke rage haɗarin kamuwa da ciwon siga ga mata.

No comments