Ko Kun San Amfanin Habbatus Sauda Guda 31 Ga Lafiyar Dan-adam ?

A wannan makom za mu kawo mu ku wani binciken zamani kan magungunan da Habbatus-sauda ke yi ga jikinmu. Mu na fata Allah Ya sa mu dace, amin.
Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye da yawa, misali ana kiranta da"Habbatul Baraka" wato kwaya mai albarka. Da turanci kuma ana kiran ta da 'the blessed seed', Black Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu.
Binciken ya dangata habbatus-sauda da matukar amfani wajen magance cututtuka daban-daban, sannan ta na taka muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiya, cikin yardar Mai Duka.
Ana samun Habbatus-sauda daga 'ya'yan tsiron "Nigella sativa". Hakanan an gano cewa, Shekaru aru-aru da suka gabata dubun-dubatar al'ummar nahiyar Asia da Afirka ke amfani da ita a fannin kiwon lafiya da kuma magance wasu cututtuka dake addabar jikin dan-adam.
Ba tare da bata lokaci ba, ga jerin magunguna 31 da ake samu daga wannnan tsiro mai albarka, da fatan a sha karatu lafiya, sannan da fatan za'a jarraba domin gane wa ido amfaninta.
1. Habbatus sauda Na Maganin Matsalar Tsakuwar Koda/Mafitsara; Ana amfani da Habbatus Sauda domin fitar da tsakuwar koda ko ta mafitsara. Yadda za a hada wannan maganin shine, a samu habbadus sauda mai kyau, da kuma zuma marar hadi, sai a cakuda su sannan a zuba ruwan zafi a rinka sha. Da yardar Allah za a samu waraka. Hakanan za a iya amfani da wannan hadin don kawar da matsalar fitsari musamman ga maza tsofaffi dake fama da wannan matsala.
2. Habbatus sauda Na Maganin Ciwon Kai; An tabbatar da cewa, habbatu sauda na magance ciwon kai. Domin samun wannan fa'ida sai a hada garin habbatus-sauda da ruwan Kal, ake sha sannan kuma a dinga digawa a hanci don samun afuwa daga matsanancin ciwon kai.
3. Habbatus sauda Na Samar Da Isasshen Ruwan Nono Ga Mace Mai Shayarewa; Wani lokacin akan samu mace ta haihu amma kuma ta rasa isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta, idan har haka ta kasance, sai a samu garin habbatus-sauda a hada ta da madara, mace mai shayarwar ta rinka sha, idan Alllah Ya yarda za ta samu isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta.
4. Habbatus sauda Na Maganin Tsutsar Ciki; Habbatus-sauda na maganin tsutsar ciki. Ga duk mai fama da wannan matsala sai ya samu garin habbattus sauda ya gauraya ta cikin ruwan kal ya ke sha.
5. Habbatus sauda Na Kara karfin Garkuwar Jiki; Wani bincike da wasu masana su ka gudanar kan habbatus-sauda ya tabbatar da cewa, yawan amfani da ita na da matukar muhimmanci wajen karawa garkuwar jikin dan adam karfi.
6. Habbatus sauda Na Rigakafin Kamuwa Daga Cututtuka; Wani bincike ya gano cewa, yawan amfani da Habbattus-sauda wata hanya ce ta magance duk wata cuta da ka iya yiwa jikin dan Adam barazana. Ta na yin wannan aiki ne ta hanyar samar wa da jikinmu garkuwa mai karfi ta yadda cutukan da kan kai wa jiki hari ba za su iya tasiri gare shi ba.
7. Habbatus sauda Na Dakile Yaduwar Kwayoyin Cuta Cikin Jiki; Hakanan wani bincike da aka gudanar kanta ya bayyana cewa, ta na dakile girman kwayoyin ccuta a jikin mutum, baya ga haka ta na hana yaduwar kwayoyin cutar ga sassan jikinmu.
8. Idan mutum na fama da yawan rashin lafiya, ya samu madara kofi daya, kyakkyawar zuma marar hadi babban cokali uku, da kuma garin habbatus-sauda babban cokali daya, sai a hada su a cakuda su sosai, sannan yake sha kullum, Insha Allahu zai samu afuwa daga ciwon, baya ga haka kuma jikin mutum zai samu kuzari.
9. Habbatus sauda Na Maganin Gyambon Ciki; Ga wanda ke fama da wannan larura sai ya samu garin hulba , da garin habbatus-sauda , da zuma, ya hada su waje guda ya gauraya su , sannnan ya dinga sha da safe , kafin ya ci komai, kuma idan ya sha kar ya karya sai bayan awa daya. Haka zai yi da rana , da dare. Hakanan idan ya so zai iya samun man hulba ya dinga sha da zuma. In sha Allahu zai sami waraka.
10. Habbatus sauda Na Maganin Asma; don samun wannan fa'ida sai a zuba man habbattus-sauda digo 5 zuwa 15 (gwargwadon shekarun wanda zai amfani da ita), a cikin shayi ko tafashashen ruwa a ke sha.
11. Habbatus sauda Na Maganin Ciwon Kunne; Ana amfani da habbatus-sauda wajen magance ciwon kunne. Abubuwan da mutum zai tanada sune, kwayar habbatus-sauda, man habbatus-sauda da kuma man zaitun.
Yadda za ka hada shine, tun da farko za ka soya kwayar habbatus-sauda sama-sama sannan sai ka nike ta don ka sami garinta, sai ka hada da rabin cokali na man habbatus-sauda da kuma rabin cokali na man zaitun ka gauraya su da kyau. Bayan ka tabbatar sun hadu, sai ka adana wannan hadi cikin mazubinka mai tsafta wanda kuma yake da murfi gudun kar ya zube.
Yadda za kai amfani da shi kuwa shine, sai ka samu sirinji ka ke yin amfani da shi wajen digawa a kunne sau biyu a rana.
12. Habbatus sauda Na Maganin Zubewar Gashi; Wasu matan kan fuskanci matsalar zubar gashin kansu. Ga masu fama da wannan matsala za su iya yin amfani da habbatus-sauda wajen magance wannan matsala. Sai dai a nan za a yi amfani da man habbatus sauda ne ba da garinta ba. Yadda za a yi shine a samu man habbatus sauda da man zaitun ma su kyau, sai a hade su waje guda. Sai ki tsefe gashin ki shafe kan da wannnan hadi na man habbatus sauda da na zaitun, sai ya na da kyau ki tabbatar man ya samu gindin gashin sosai.
13. Ana Amfani Da Habbatus sauda Wajen Gayaran Fata; Habbatus sauda ta shahara kwarai da gaske wajen gyaran fata. Tuni aka jarraba wannan hadi mai sauki kuma aka ga fa'idarsa. Wannan hadi ba shi da wata wahala kamar yadda muka ambata a sama. Za ki samu garin habbatus sauda ki hada da man zaitun ki cakuda su waje huda, sai ki shafa wannan hadin a fuskar ki, za ki jira har misalin awa daya sannan ki wanke. Matukar ki ka juri yin amfani da wannan hadi na habbatus sauda to fuskarki za ta yi sumul, sheki da kuma taushi.
14. Habbatus sauda Na Inganta Karfin Garkuwar Jikin Dan-adam; Habbatus sauda na taimakawa wajen kara karfin garkuwar jikin bil adama. Ga mai son samun wannan fa'ida ta habbatus sauda, sai ya samu man habbatus sauda mai kyau ya adana, ya juri shan rabin cokali a kullum.
15. Habbatus sauda Na Maganin Tsutsar Ciki; Habbatus sauda na magance matsalar tsutsar ciki, don samun wannan fa'ida mutum zai samu garin habbatus sauda ya hada da ruwan khal, ya ke sha sau uku a kullum.
16. Habbatus sauda Na Maganin Rauni Ko Ciwo; Domin samun wannan fa'ida ta habbatus sauda, mutum zai shafa a saman ciwon ko raunin, da iznin Allahu( S.W.T) za’a samu waraka.
17.Habbatus sauda Na Maganin Kunan Wuta; Kamar yadda take amfani da ita wajen warkar da rauni ko ciwo haka kuma ake amfani da habbatus sauda wajen warkar da kunan wuta. Idan har tsautsayi ya faru mutum ya kone zai yi amfani da habbatus sauda kamar yadda zai yi akan rauni ko jin ciwo, wato ya shafa a saman kunan.
Karin wasu magungunan da Habbatus-sauda ke yi sun hada da:
18. Habbatus sauda Na Maganin matsalar Jinin al’adar Mata.
19. Habbatus-sauda na samar da kuzarin jiki.
20. Ana amfani da habbatus sauda wajen gyaran Fata
.
21. Ana amfani da Habbatus sauda Wajen Maganin matsanancin tari Da Mura.
22. Ana amfani da habbatus sauda wajen maganin Ciwon Ciki; Anan za ayi amfani da man Habbattus-sauda ne.
23. Habbatus sauda na maganin ciwon shanyewar bangaren jiki.
24. Ana sarrafa habbatus sauda wajen maganin yanar ido.
25. Habbatus sauda na rage nauyin jiki ga masu kiba ko teba.
26. Habbatus sauda na maganin ciwon zuciya.
27. Habbattus-sauda na saukar da hawan jini.
28. Gyaran Gashi.
29. Habbatus sauda na Kara yawan maniyyi.
30. Magance Cutukan Fata.
31. Man Habbatus sauda na magananin ciwon ciki.
Madogara: www.mujalla.com.ng
No comments