Mai karatu barka da wannan lokaci, a wannan makon za mu duba irin fa'idojin da Karas ke da su ga lafiyarmu. Masana a fannin kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, karas na kunshe da wasu sanadarai ma su matukar muhimmanci wajen inganta lafiyar dan-adam. Misali daga cikin sanadaran da karas ke kunshe da su akwai sinadarin "Bitamin A", wanda ke taimaka wa wajen inganta karfin gani.
Kai, al'amarin bai tsaya ga karin gani ba, Karas kan ba da gudummuwa wajen inganta lafiyar kwayar idon mutum, akwai masana da yawa a fagen da ya shafi magani daga tsirrai da su ka gudanar da bincike, wasu kuma sun yi wallafe-wallafe kan amfanin Karas ga lafiyar dan-adam, kuma sun tabbatar da cewa ba karamar gudunmawa Karas ke bayar wa ba ga inganta lafiyar ido.
Baya ga haka manazarta da yawa, sun bayyana cewa, Karas na kunshe da wani sanadari da ake kira da 'Beta Carotene' a turance, wanda yakan taimaka wajen karfafa garkuwar jiki, ya na taimaka wa wajen rage hadarin kamuwa da wasu cututtuka kamar cututtukan da kan shafi zuciya, da matsalolin jini, da matsalolin ido kamar yadda bayani ya gabata.
Hakanan, Karas na taimaka wa wajen gudanar da fitsari, ya na samar da gwargwadon sanadarin 'Nitrogen' da jikin dan adam ke bukata, baya ga taimaka wa wajen maganin matsalolin kashi, da ciwon gabobi.
Mu na kyautata zaton cewa, ko iya nan mu ka tsaya, ba shakka mai karatu ya san, Karas na da matukar amfani ga lafiyar dan-adam. Yanzu za mu jero wasu daga cikin amfanin Karas ga lafiyarmu tare da bayanin yadda za ayi amfani da Karas don samun fa'idojin da Allah (S.W.T) ya kimsa cikinsa.
Gyaran Fata.
1. Binciken masana kiwon lafiya ya nuna yadda Karas ke kunshe da sanadaran 'Antioxidants', kuma sakamakon haka ne su ka bayanna yadda yake iya maganin tauyewar fata da ke nuna alamar tsufa.
2. Hakanan dai, dangane da fata ana yi wa karas kirari da 'Mai da tsohuwa yarinya', ma'ana ya kan gyara fata ta kasance danya a kowanne lokaci. Dalili shine yana rage tsufan fata. Domin samun wannan amfani sai a markada karas, sannan a ke sha ruwan a kowacce rana.
3. Ko kuma, don mutum ya samu wannan fa'ida ta Karas, ya samu karas ya tafasa shi sannan ya nike shi ya hada da kindirmo. Daga nan sai ya shafe fuska da wanan hadi na karas ya tabbatar ya game fuskarsa da shi, ya kyale shi tsawon mintuna 5 zuwa 10 daganan sai ya wanke.
4. Wata hanyar ta samun fa'idar karas game da gyaran fata shine, mutum zai samu karas ya nike shi ya hada shi da man Zaitun da zuma ya cakuda ya tabbatar sun hadu sosai, sai ya shafe fuskarsa da wannan hadi na karas, ya jira tsawon mintuna 15 sai ya wanke da ruwan dumi. Da sannu za a ga abin mamaki.
5. Ga ma su fama da tabon fuska ko kuma fama da wata cutar fata, za su iya amfani da karas wajen samun waraka. Abin da za su yi shine, su markada karas sannan su ke shan ruwan, hakan na sanya tabon fuska ya dusashe sannan kuma a rabu da cutar fata cikin sauri.
6. Hakazalika Shan ruwan markadadden karas wato jus din karas, musamman a lokacin zafi na taimakawa wajen magance dabbare-dabbaren fuska sakamakon tsananin zafi. Haka na faruwa ne lokacin da mace ta yi tafiya a rana, sai ka ga fuskarta ta yi wani dabbare-dabbare ma'ana launi daban-daban. Yawaita shan jus din karas a lokacin zafi na magance wannan matsala.
7. Masanan sun gano cewa, sakamakon sinadaran da karas ke kunshe da su, yana taimakawa wajen magance kurajen fuska wato 'finfus' da makamantan kurajen fuska. Binciken ya kara da cewa, jama'a musamman matasa maza da mata na fama da wannan larura ta fesowar kurajen ne sakamakon karancin sinadarin bitamin A a fata. Don haka su ka tabbatar da cewa cin karas na magance wannan matsala.
8. Hakazalika, za a iya magance wannan matsala ta fesowar kurajen fuska ta hanyar markada karas sai a hada shi da madara da man zaitun kadan da zuma, sannan a kwaba su sosai, a shafa a fuska a kyale shi kimanin tsawon mintuna 30, sannan a wanke. Hakan na magance fesowar kurajen fuska.
9. Har ila yau masana sun bayyana cewa, Karas na bai wa dan-adam kariya daga barazanar kamuwa da cututtukan hanta.
10. Haka dai an gano cewa ya na Kara lafiyar hakora, da Kuma dadashi.
11. Rigakafin kamuwa da tsutsar hakori ne.
12. Baya ga haka yana taimakawa wajen magance warin baki.
13. Yawan cin Karas na kara karfin kashi.
No comments