Wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki, Uwar-gida Toyin Aliu, ta fada a Kwalejin Kimiyya da fasahar Lafiya, dake Offan, jihar Kwara, cewa, amfani da rubabben tumatir, na iya haifar da ciwon daji.
Aliu, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a wata tattaunawa ta wayar tarho, a ranar Talatar da ta gabata a Offa, cewa, yayin da tumatir ya rube akwai wasu kwayoyin halitta da su ke rikidewa zuwa kwayoyin cuta, kuma su kan iya yin lahani ga jikin mutum matukar ya yi amfani da wannan tumatir da ya rube.
"Yin amfani da rubabben tumatir zai iya haifar da cutar daji, domin kuwa matukar tumatir ya rube, ya na samar da kwayoyin cuta wanda, mafi yawansu ake kira 'fungi' da turanci.
"Fungi dake cikin rubabben tumatir shi ke samar da wasu kwayoyin cuta da ake kira 'mycotoxins' a turance, wadanda suke da matukar hadari a jikin mutum saboda su na iya haifar da ciwon daji, kuma baya ga haka za su iya karya garkuwar jikin dan-adam.
"Tun da mafi yawan tumatir ya na ƙunshe da ruwa ne mai yawan gaske, su wadannan kwayoyin na 'mycotoxins' su kan rubanyu a cikin rubabben tumatir, sannan su game dukkan sassansa, saboda haka yake da matukar hadari a yi amfani da shi wajen giki," inji Aliu.
A cewarta, da zarar tumatir ya rube, ya kan zama matattarar tsutsotsi wanda kuda ke haifar ta hanyar saukarsa akansa, sakamakon haka ta yi kira ga jama'a kan su guji mu'amala da rubabben tumatir wajen girke-girkensu na yau da kullum.
Kwararriyar ta kara da cewa, duk da cewa, rubabben tumatir ya fi rahusa wajen saye a kasuwa, sai dai yana da kyau jama'a su ke sayen kyakkyawan tumatir maimakon yin amfani da tumatirin da ya rube don kuwa cin irin wannan tumatir tamkar cin guba ne.
"Mummunan sakamakon cin rubabben tumatirin na bayyana ne sannu a kan hankali, don haka ba da zarar mutum ya ci ne, illar za ta bayyana ba.
"Saboda haka, ya fi kyau mu ci abin da muke da tabbacin lafiyarsa koda yana da tsada maimakon cin abu mai araha wanda kuma daga baya za mu yi dana-sanin cin sa da mu ka yi," inji Aliu.
No comments