Breaking News

Amfanin Ayaba Guda 8 Ga Lafiyar Dan Adam





A matsayin ayaba na kayan marmarin da ta yi fice ba ta bukatar wani karin bayani ga mai karatu. Saboda ayaba tana daya daga cikin kayayyakin marmarin da mutane ke ci yau da kullum.  Sai dai mafi yawan mutane na cin ayaba ne, saboda dadin ci, musamman yadda ta ke da laushi da kuma zaki. Amma mutane da ke cin ayaba ba su san cewa, ta na amfani ga lafiyarsu ba.

Sakamakon haka ne, shafinku mai farin jini na "Lafiyar Iyali" ya kawo mu ku wannan makala mai taken "Amfanin Ayaba Ga Lafiyar Dan-adam"

Ayaba na daya daga cikin kayan marmari da ke da saurin samarwa jikin mutum kuzari. Hakanan ayaba na kadan daga cikin kayan marmari da ake iya samu  shine ko'ina a fadin duniya.  Misali a kasar Indiya, su na ba ta muhimmancin gaske inda wurare daban-daban na kasar ke amfani da ayaba a don samar da abinci na'ika daban-daban, kamar, kheer, malpua, halwa, payasam, sheera, da paniyaram, da sauran su.

Haka al'amarin ya ke a yankunan gabashin Duniya da kuma arewa maso gabas, su kan lizamci yin  karin kumullo da ita. Idan ka shiga shagunan sayar da abinci a wadannan yankuna, za ka tarar da cewa, ayaba na daya daga cikin abincin da suke hadawa cikin abincin saafensu.

Karanta: Amfanin Tafarnuwa Ga Lafiyar Bil'adama

Daga cikin dalilan da ya sa, su ke damuwa da cin ayaba da safe shine, yadda masana su ka tabbatar da cewa, cin ayaba na samarwa jiki kuzari, mutum zai fita harkokinsa cikin walwala da kuzari.  Wani nazari da aka gudanar kan amfanin ayaba ga lafiyar dan adam ya gano yadda ta ke kunshe da wani sanadari da ke saurin samarwa jiki kuzari da gaggawa.

Baya ga haka binciken ya bayyana yadda za a iya amfani da ayaba wajen maganin matsalolin ciki, da su ka hada da cushewar ciki, da rashin narkewar abinci da sauran su. Misali a kasar Indiya, su kan yi amfani hada ayaba da wasu abubuwa don maganin matsalolin ciki da yawa.

Yanzu ba tare da bata lokaci ba, ga wasu daga cikin amfanin ayaba ga lafiyar dan adam, da fatan a sha karatu lafiya, kuma Allah Ya sa mu dace, amin.

1. Inganta Lafiyar Zuciya.

Wani bincike da nazari da masana su ka gudanar kan amfanin ayaba ga lafiyarmu, ya gano cewa, ayaba na kunshe da sandarin 'Fibre' mai yawa, wanda haka ya sanya cin ta akai-akai kan inganta lafiyar zuciya. Mafi yawan kayan abinci da ke kunshe da wannan sandari na 'fiber'  suna da muhimmmanci ga zuciya. Bisa ga wani bincike da Jami'ar Leeds ta kasar Burtaniya ta gudanar, ya nuna cewa, yawan amfani da abinci mai kunshe da sanadarin fiber-irin su ayaba na iya ragewa mutum haÉ—arin kamuwa da cututtukan zuciya.

Karanta: Amfanin Jima'i Ga Lafiyar Ma'aurata

2.  Saurin Narkewar Abinci.

Manazarta, sun tabbatar da cewa, daga cikin amfanin ayaba ga lafiyar adam, akwai taimaka wa wajen saurin narkar da abinci. Saboda haka ne, su ka bada shawara ga jama'a su yawaita cin ayaba don su sami lafiyar cikinsu, da ma sauran jikinsu gaba daya, saboda saurin narkar da abinci na sanya wa abinci ya yi tasiri a jikinmu cikin gaggawa.

3. Hawan Jini

Ya tabbata cewa, ayaba na taimakawa mutnen dake fama da hawan jini, sakamakon yadda ta ke kunshe da wani sanadari mai suna 'potassium' sannan sun tabbatar ba ta da sanadarin gishiri mai yawa a cikinta, wannan dalilin  yasa take taimakawa wajen daidaitawa tare da saukar da hawan jini.

Wannan dalilin ne ya sa, Hukumar kula da kiyaye tsaftar abinci da magunguna ta kasar Amurka ta himmatu wajen wayar da kan jama'a kan amfanin da ayaba tsakanin 'yan kasar. Hakanan, ta taimaka wajen sahalewa kamfanonin kasar shigo da Ayaba cikin kasar daga kasashen ketare, ba don komai ba, sai don yadda hukumar ta fahimci cewa yawan cin ayabar na bada kariya daga kamuwa da hawan jini da kuma mutuwar sashen jiki.

4. Kara Kaifin Basira.

Wani amfanin ayaba ga lafiya da masana su ka gano shine, kara lafiyar kwakwalwa da kuma kara kaifin basira. Kamar yadda mu ka ambata a sama cewa,  ayaba na kunshe da sanadarin 'potassium' mai yawa, wanda bincike ya nuna shi wannan sanadari taimakawa kwakwalwar yara ta kasance mai basira da saurin tuna al'amuran da aka shaida mu su.

5. Maganin Gyanbon Ciki.

Daga cikin misalin da mu ka bayar a farkon wannan takarda, dangane da amfanin ayaba ga lafiyar bil'adama, mun bayyana yadda mutanen kasar Indiya ke amfani da ita wajen dakile matsalolin ciki, tun a shekarun baya da su ka gabata. Sakamakon haka ya sa, a wannan lokaci ake amfani da ayaba a matsayin maganin gayambon ciki. Wannan kuwa ya hada da irin zafin cikin nan da ma su gyambon ciki ke fuskanta, da gyambon ciki da ke shafar hanji, da kuma uwar hanji.

Karanta: Amfanin Man Kwakwa Guda 11 Da Ba Kowa Ya Sani Ba

6. Ayaba Na Kunshe Da Sanadaaran Gina Jiki.

Bincike ya tabbatar da cewa, ayaba na kunshe da sanadaran gina jiki da ba kowannne abinci ke kunshe da su ba.  Masanan sun bayyana cewa, ayaba na kunshe da muhimman sanadiran gina jiki da su ka hada da, potassium, calcium, manganese, magnesium, iron, folate, niacin, riboflavin, da kuma Vitamin B6. Dukkan waÉ—annan sanadarai na taimakawa wajen inganta aikin jiki da kuma tabbatar da cikakkiyar lafiyar jikin dan-adam.

7. Ayaba Na Inganta Lafiyar Koda.

Babu shakka bincike ya gano cewa, ayaba na iya inganta lafiyar koda. Sanadarin 'Potassium' dake cikin ayaba, na da muhimmanci wajen daidaita hawan jini da kuma inganta lafiyar koda da kuma aikinta.

Saboda haka ne, binciken ya nuna, a matsayin ayaba na kyakyawan tushen sanadaran potassium, hakan ya sanya ta kasance mai matukar mahimmanci don kiyayewa tare da inganta lafiyar koda.

Wani daga cikin bincike da manazarta su ka gudanar shekaru 14 da su ka gabata ya tabbatar da cewa, mutanen da ke cin ayaba sau 2 zuwa 3 a kowanne mako suna samun kariyar kamuwa da ciwon koda har kashi 33 cikin 100, idan aka kwatanta su da wanda ba su cin ayaba kamar su.

Wani binciken kuma ya nuna cewa, mutanen da ke cin  ayaba sau 4 zuwa 6 a mako suna samun kariya daga kamuwa da ciwon koda har kashi 50 cikin 100 fiye da wadanda basu cin wannan 'ya'yan itace.

Karanta: Maganin Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada

8.  Taimakawa Wajen Rage Kiba.

Duk da cewa, zuwa wannan lokaci masana sun ce, babu wani binciken kimiyya da ya danganta ayaba da rage kiba, sai dai duk da haka, suna ganin ayaba na kunshe da wasu nau'o'in sanadarai da ka iya taimakawa wajen  rage kiba.

Abinda su ka ce shine, bincike ya tabbatar da cewa, ayaba na kunshe da adadi sandarin 'Clories' kaÉ—an a cikinta.  Misali sun ce, matsakaciyar ayaba na kunshe da adadin sanadarin clories  sama da 100  ne kawai - duk da haka tana da mahimman sanadaran gina jiki da suka hada da 'fiber'.

Cin kayan lambu da 'ya'yan itatuwa masu kunshe da sanadarin 'fiber' akai-akai,  kamar ayaba na da danganta da rage nauyin jiki da kuma kiba ko teba.

Bugu da Æ™ari, binciken ya nuna cewa,  ayabar da ba ta nuna ba, na kunshe da wani sanadari da ake kira,  'starch'  da turanci, wanda ke hana mutum jin yunwa kuma ya hana shi sha'awar cin abinci da gaggawa.

Karanta: Yin Girki Da Rubabben Tumatir Na Haddasa Cutar Daji

No comments