Amfanin zuma ga lafiyarmu ba shi misaltuwa, sai dai mutum ya bayyana iya wanda Allah Ya sanar da shi. Tun a karnoni daban-daban da su ka shude al'ummomin duniya ke amfani a zuma wajen samun waraka da kuma riga-kafin kamuwa daga wasu cututtuka. Baya ga haka har a wannan zamanin masana sun gudanar da bincike kan amfanin zuma ga lafiyar dan-adam, kuma wasu na kan gudanar da bincike domin gano krin magungunan da za'a iya samu daga zuma.
Hakanan, masana'antun da ke sarrafa magungunan zamani na yin amfani da zuma wajen samar da magungunan cututtuka daban-daban, baya ga kamfunan dake amfani da zuma a wasu mayukan gyaran jiki da sauran su.
Wadannan al'amura ba abin mamaki ba ne gare mu Musulmi saboda tuni Allah (S.W.T) Ya bayyana ma na cewa, zuma magani ce, wato dai ana samun waraka daga gare ta.
Allah (S.W.T) ya fada a cikin Al'qur'ani mai girma "Kuma ubangijinka Ya yi wahayi ga kudan zuma cewa; Ki riki gidaje daga duwatsu, kuma daga itace, kuma daga abin da suke ginawa".
"Sa'an nan ki ci daga dukkan yayan itace,saboda haka ki shiga hanyoyin Ubangijinki, suna horarru". Wani abin sha na fita daga cikunanta, mai sabawar launukasa, a cikinsa akwai wata waraka ga mutane. Lalle ne cikin wannan hakika, akwai Ayoyi ga mutane wadanda suke yin tunani" (Qur'an: Suratul Nahl(16) Aya ta 68-69).
Hakanan, Manzon Allah (S A W) Ya ce, "Na hore Ku da abubuwan waraka guda biyu , zuma da alkur’ani".(ibn majah da Hakim suka ruwaito)
Abu Sa'idul Khudri (R.A) ya ce "Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (S.A.W) ya ce dan-uwana yana fama da ciwon ciki. Sai Manzo (S.A.W) ya ce Ya sha zuma. Mutumin ya sake dawowa karo na biyu, Manzo Allah (S.A.W) ya sake ce masa ya sha zuma. Ya sake dawowa karo na uku, Manzo (S.A.W) Ya sake cewa da shi ya sha zuma. Mutumin ya sake dawowa ya ce na aikata abin da ka ce (amma bai warke ba ). Sai Manzon Allah (S.A.W) Ya ce Allah Ya yi gaskiya cikin dan-uwanka ya yi karya, ya sha zuma. Ya umarce shi da shan zuma kuma ya warke" (Bukhari).
Kamar yadda mu ka ambata tun a farkon wanan makala cewa, amfanin zuma ga lafiyar dan-adam ba zai kidayu ba, kuma mun san mai karatu zai amince da wannan batu namu saboda yadda Allah (S,W,T) da kanSa ya bayyana cewa ana samun waraka daga gareta kuma bai kayyade cututtukan da ta ke warkarwa ba. Hakanan ManzonSa (S.A.W) Ya tabbatar da magani ce.
Daga cikin amfanin zuma ga lafiyar dan adam, bincike ya tabbatar da cewa zuma na maganin mura, ana amfani da zuma wajen gyaran fata, Zuma na kuma warkar da rauni ko kuma kuna a jikin mutum. Zuma na maganin ciwon ciki, cushewar ciki, gyambon ciki da sauran matsalolin ciki. Ana amfani da zuma wajen maganin karin basira, da sauran magunguna.
Yanzu za mu kawo wa mai karatu jerin amfanin zuma ga lafiyarmu, gwargwadon yadda Allah(S.W.A.) Ya sanar da mu. Sannan za mu yi bayanin yadda za'a sarrafa zumar don samun fa'idarta. Da fatan za ai karatu lafiya, Allah Ya sa mu dace.
1. Maganin Mura.
Binciken masana kiwon lafiya ya tabbatar da cewa, daga cikin amfanin zuma ga lafiyarmu, akwai maganin mura, tari, kaikayin makogwaro, yawan atishawa, yayyon hanci da suuran matsalolin da ke da dangantaka da mura.
Yadda mutum zai yi don samun waraka daga wadannan matsalolin lafiya da mu ka ambata, sai ya samu, zumarsa mai kyau marar gauraye, da tafarnuwa, da citta, da lemon tsami. Bayan ya samu wadannan kayan hadi, sai ya dafa shayi da sauran kayan hadin ban da zuma, daga bisani ne zai zuba zumar ya ke sha. Zai samu sauki in sha Allahu.
2. Maganin Gyambo Ko Kuna.
Daga cikin amfanin zuma ga lafiya, akwai maganin gyambo ko kuma kunan wuta. Mutum zai samu waraka daga wadannan matsaloli matukar ya na shafa zuma mai kyau a wajen da ciwon ya ke. Sannan kuma ya ke sha. Wato abin nufi zai ke shan zuma, sannan ya na shafa zumar a kan ciwon.
3. Gyambon Ciki.
Hakanan, bincike ya nuna cewa, daga cikin amfanin zuma ga lafiyar dan adam har da maganin gyambon ciki. Ga mai fama da wannan larura ta gyambon ciki, kuma ya ke son samun waraka ta yin amfani da zuma, sai ya samu zuma mai kyau marar algus, ya hada ta da hulba da ruwa zafi tafasasshe, sai ya bari bayan ya huce tukuna, sannan kafin ya ci abinci sai ya sha.
Hakazalika daga irin amfanin da zuma ke da shi ga lafiya, akwai hana warin baki. Idan mutum na fama da wannan matsala ta warin baki, ya kan rasa sakewa cikin jama'a, za ka gan shi duk lokacin da ya ke son magana cikin abokan hirarsa sai ya na kawar da kansa, don kar su ji warin da bakinsa ke yi. Don rabuwa da wannan matsala sai ya ke shan zuma kullum da safe. Zai rabu da warin bakin, in sha Allahu.
5. Gyaran Fata.
Daga cikin amfanin zuma ga lafiya, akwai gyaran fata, idan mace na son samun fata mai kyau da taushi, sai ta gyara fatarta da zuma. Saboda zuma na maganin bushewar fata, sanan zuma na sa fata ta ke sheki, baya ga haka zuma na maganin kurajen fuska.
Don maganin cutukan fata irin su kyasbi, makero ko finfus, ki samu zuma da kirfa (cinnamon) sai ki Hade su waje guda ki shafa a fuskarki, ki bar su tsawon mintuna 10 zuwa 15, sannan ki wanke da ruwan dumi. Matukar ki ka dimanci amfani da wannan hadin za ki ga yadda fuskarki za ta canza cikin karamin lokaci, don kuwa zai sa fatarki ta kasance cikin sheki da kuma damshi.
Ko kuma, ki samu zuma da lemon tsami ki hada, bayan haka sai ki shafa a fuskarki. Shi ma wannan hadin ya na maganin kurajen fuska da tabo sannan ya nasa fuskar tayi sumul da sheki, abar sha'awa.
Hakanan, ga wani hadin, shi kuma za ki, samu zumarki mai kyau maras algus sai ki hada ta da 'yoghurt' amma wanda ba ta da flavor a ciki, sai ki shafa a fuskarki ki jira tsawon mintuna 20 sannan ki wanke, wannan hadi na sa fuska ta yi kyau. Hakazalika shi ma wannan hadin na kawar da kuraje fuska da kuma gusar da tabo.
Idan mutum na fama da wadannan matsaloli da mu ka ambata a sama, sai ya samu tacacciyar zuma mai kyau marar gauraye, cikin babban cokali daya(1) sannnan sai ya samu tafarnuwa, ya marmashe ta- mun san tafarnuwa sala-sala ta ke- to sai ya ciri sala uku daga ciki, ya dandaka ta, sai ya hada ta da zumarsa babban cokali daya, ya ke sha kullum da safe kafin ya ci abincin. Haka zai yi har tsawon mako guda. In sha Allahu zai samu waraka.
7. Maganin Rage Kiba.
Har-ila-yau, daga cikin amfanin zuma ga lafiya bil'adama, har da maganin rage kiba/teba. Wasu mutane kan yi fama da yawan kiba, har abin ya dame su, saboda wani lokaci jikinsu kan yi nauyi, kuma ko ba komai ana danganta wasu cututtuka da yawan kiba.
To idan mutum na son ya rage kiba, sai ya samu zumarsa mai kyau marar algus da lemon tsami, sai ya ke matsa ruwan lemon tsami cikin ruwan`dumi, sannan ya zuba zumarsa ciki ya ke sha da safe kafin ya ci komai. Wannan hadin na taimakawa kwarai da gaske wajen rage kiba.
8. Saurin Narkar Da Abinci.
Amfanin zuma ga lafiyar dan adam ya hada da taikamawa wajen saurin narkar da abinci musamman mai nauyi. Ba shakka zuma na saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci. Ga mai fama da wannan matsala sai ya yi takidin zumarsa mai kyau, da zarar ya kammala cin abinci sai ya sha zumar.
Wani bincike da masana kiwon lafiya su ka gudanar kan amfanin zuma ga lafiya, ya nuna cewa, ta na iya karawa mutum kuzari. Wani lokacin sai ka ji kasala na damun ka ba tare da wani dalili ba. Domin samun kuzarin jiki kuma ka rabu da yawan kasala, sai ka samu zuma tacaccaciya marar hadi ka ke shan cokali daya(1) kullum da sassafe kafin ka karya.
10. Inganta Garkuwar Jiki.
Daga cikin amfanin zuma ga lafiyarmu, akwai kara karfin garkuwar jiki don yakar cututtuka da kan kaiwa jiki farmaki, kuma ta yi galaba kansu. Masana kiwon lafiya, sun tabbatar da cewa, Zuma na samarwa jiki wasu sinadarai wandanda ke kara karfin garkuwar jikin dan-adam.
11. Zuma Na Kara Basira. Yawan shan zuma na karawa mutum basira, da hana shi yawan mantuwa.
12. Zuma na rage hadarin kamuwa daga cutar daji. Saboda haka idan mutum ya dimanci amfani da zuma, ta na rage ma sa yiwuwar kamuwar daga cutar daji.
13. Har-ila-yau dai daga amfanin zuma ga lafiyarmu, har da karin karfin kashi.
No comments