Ba shakka, Kokwamba ta yi fice wajen inganta lafiyar dan-adam, musamman saboda sanadiran gina jiki da kokwambar ke da su, kamar yadda masana su ka bayyana. Misali wani bincike da aka gudanar kuma aka wallafa a shafin yanar gizo na "Healthline" ya nuna cewa, kokwamba na dauke da sanadaran, 'Calories', Protein, Fiber, Vitamin K, Da na C, Magnesium, Potassium,da kuma Manganese.
Baya ga haka binciken ya nuna cewa, kashi 96 na kokwamba ruwa ne, kuma ba sai an fada ba, mai karatu ya san yadda ruwa ke da matukar amfani wajen inganta lafiyar dan adam.
Saboda haka ne a wannan rana mu ka kawo wa mai karatu amfanin kokwamba guda 19 ga lafiyar dan-adam. Da fatan a sha karatu lafiya kuma Allah Ya sa mu dace, amin.
Kowa ya san irin muhimmancin da ruwa ke da shi a jikin dan-adam. Saboda haka ne, da zarar ruwan jikin mutum ya ragu sosai ya ke galabaita. Bincike ya tabbatar da cewa, kashi 96 cikin 100 na Kokwamba ruwa ne, sakamakon haka ta ke samar da ruwa ga jikinmu. Duk lokacin da aiki ya shagaltar da kai sosai har ka kasa samun lokacin da za ka sha ruwa mai yawa, cin kokwamba zai taimaka wajen maye gurbin ruwan da ba ka sha ba.
2. Maganin Zafin Jiki
Cin kokwamba, na maganin zafin jiki da ya hada da na cikin jiki da kuma na wajensa. Hakanan masana sun bayyana yadda shafa kokwamba a jikinka kan iya maganin lahanin da zafin rana ke yiwa fatarka, kuma hakan kan bada kariya daga matsanancin zafi da kuma kaikayin fata.
3. Fitar Da Sanadarai Ma Su Lahani Ga Jiki
Ruwa da ke cikin kokwamba yana aiki kwatankwacin na tsintsiya a gidajenmu, wajen tsabtar muhalli. To, kamar haka ne amfani da kokwamba yau da kullum, ke sanya ta tunkudo sanadarai da duk wani datti da jiki ba ya bukatar sa. Kokwamba na tsabtace mara da hanyoyin jini da koda da sauran sassan jiki.
Kokwamba na samrwa jiki sandaran Bitamin A, B da kuma C, wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyarmu. Hakanan, su wadannan sanadarai na samarwa jiki karsashi da kuzari musamman idan an hada kokwambar da karasa da ganyen kabeji.
5. Samarwa Jiki Sanadaran Gyaran Fata
Muhimman sanadarai irinsu, magnesium da potassium da kuma silicon na da yawa cikin kokwamba, kuma wadannan sanadarai sun yi fice wajen gyara fata da inganta lafiyarta. Wannan dalili ya sa kokwamba ta shahara wajen gyaran fata.
6. Taimakawa Wajen Rage Kiba
Cin Kokwamba ita kadai, ko kuma ka hada Kokwamba cikin salad ko dai wani nau'in abinci da ka ke jin dadinsa, na matukar taimakawa wajen rage kiba, da nauyin jiki.
Masana a fannin kiwon lafiya na danganta amfani da kokwamba da inganta lafiyar ido, saboda haka, ya na da kyau ka kasance mai amfani da kokwamba cikin abincinka don samun lafiyayyen ido mao kwarin gani.
8. Rage Yiwuwar Kamuwa Da Cutar Daji
Yawan cin kokwamba na rage haÉ—arin kamuwa da ciwon daji, saboda haka masana ke ba da shwarar yawaita hada kokwamba cikin abincinmu. An gudanar da bincike ka wannan aiki na kokwamba kuma sakamakon nazarin ya nuna cewa, kokwamba na da wasu sanadarai da ke iya samar wa jiki kariyar kamuwa daga ciwon daji .
9. Taimakawa Ma Su Fama Da Hawan Jini
Wani bincike da aka gudanar kan wasu mutane da ke fama da hawan jini ya nuna yadda cin kokwamba ke taimaka mu su wajen saukar da hawan jininsu.
10. Kokwamba Na Tsaftace Baki
Sakamakon ruwan da Kokwamba ke da shi, ya sa yawan cin ta ke tsaftace baki, musamman idan za kai amfani da tacaccen ruwan kokwambar, ya na magance ciwon da kan shafi dasashi, ta bar bakinka cikin koshin lafiya.
Sanadarin Silica da ke kunshe cikin Kokwamba wani sanadari ne da ke aiki mai ban mamaki, ta yadda ya ke sa gashi da farce su yi karfi da haske.
12. Maganin Ciwon Jiki Da Gabobi
Sanadaran Bitamins Da minerals da kokwamba ke kunshe da su na sanya ta ragargazar ciwon jiki da na gabobi.
13. Inganta Lafiyar Koda
Wani bincike ya gano cewa, Kokwamba na rage yawan adadin sandarin 'uric acid' a cikin jikin dan-adam, wanda hakan kuma ke taimakawa koda ta kasance cikin koshin lafiya yadda za ta gudanar da aikinta yadda ya kamata.
14. Taimakawa Ma Su Fama Da Ciwon Siga
Ba shakka kokwamba na taimakawa ma su fama da ciwon siga kwarai da gaske. Wani bincike da masana kiwon lafiya su ka gudanar ya nuna cewa, kokwamba na dauke da wani sanadari (hormone) wanda kwayoyin halitta na saifa ke bukata don samar da sandarin 'insulin' a jikinmu.
Wani sanadari da ake kira 'sterols' da turanci da ke cikin kokwamba yana taimakawa wajen rage kwalastaral mara kyau da ke cikin jini.
16. Samar Da Kuzari Ga Jiki
Yawan cin kkokwamba na samar wa jikinmu kuzari. Hakan ne ya sanya wani bincike ya gano kokwamba na korar gajiya cikin gaggawa. Hakazalika, binciken masana kan Kokwamba ya nuna cewa, mutum zai samu cikakkiyar wannan fa'ida musamman idan aka matse ruwanta aka hada da ruwan karas da na alayyahu. A takaice dai a samar da "Juice" na wadannan tsirrai guda uku da aka bayyana a sama.
17. Kokwamba Na Maganin Kurajen Fuska
Ba shakka Kokwamba na hana kurajen fuska yin tasiri a fuskarmu, yadda za ka ga wasu mutane musamman matasa fuskarsu ta yi muni ainun saboda kurajen fuska. Baya ga hana kurajen fuskar samun gindin zama, sai kuma ta sanya fuskar ta yi sumul abar sha'awa.
Ba shakka yawan amfani da kokwamba na samar da ingantacciyar lafiya, kyan jiki da kuzari. Wannan dalilin ne ya sa, wasu daga cikin mata da suka san wannan sirri na kokwamba ke yawaita sanya ta kan fuskarsu bayan sun rede fatarta. Ko ka san dalilin yin haka, dalili a nan shine, yayin da mace ta sanya kokwamba a kan fuskarta, kokwambar za ta tsotse duk wani kitse marar kyau da ke tattare a kan fatar fuskarta, saboda wasu sinadaran da kokwambar ke da su da ke kawar da irin wadannan cutukan fata.
19. Maganin Gajiya
Sakamakon ayyuka da zirga-zirgarmu na yau da kullum, jikinmu kan yi nauyi ko kasala sakamakon gajiya da ayyukan ko sauran harkokin neman abincinmu su ka haifar ma na. Duk lokacin da ka fuskanci irin wannan matsala kai tsaye nemi kokwamba, da zarar ka yi amfani da ita sannu kan hankali za ka ji ka nemi gajiyar ka rasa.
Hakanan, wani bincike da aka wallafa kan yadda kokwamba ke iya korar gajiya daga jikin mutum, an gano cewa, ga duk ma su fama da matsalar nauyin jiki musamman lokacin da su ka tashi daga barci da safe, to sai su ke cin kokwamba kafin su kwanta barci, da yardar ALLAH, za su wayi gari ba tare da wannnan matsala ba, don kuwa jikinsu zai kasance garau ba wani sofanen gajiya ko nauyin jiki.
No comments